Hare-haren 'yan Boko Haram a Kamaru | Labarai | DW | 22.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren 'yan Boko Haram a Kamaru

Mayakan Boko Haram sun kai hare-hare har sau uku cikin sa'o'i 24 a Jamhuriyar Kamaru ciki kuwa har da wani harin kunar bakin wake da bai yi nasara ba a sansanin 'yan gudun hijira na Kolofata.

Duk da cewa an ci karfin 'yan kungiyar sakamakon ayyukan da sojojin Najeriya da ma rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa mai sojoji dubu 10 ke yi, amma kuma tsirarun mayakan na Boko Haram na aikata ayyukan ta'addanci a kasashen Kamarun da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar masu makwabtaka da Najeriya.

A wani rahoto da ta wallafa a wannan wata na Nuwamba, kungiyar Crisis Group da ke sa ido kan rikice-rikice ta ce 'yan Kamaru fiye da mutun 1,500 ne suka mutu sakamakon hare-haren ta'addanci na 'yan kungiyar. Hari na baya-bayan nan an kai shi ne ga wani barakin soji da ke tsibirin Darak, inda sojoji shida da farar hula guda suka mutu sannan wasu hare-haren an kai su ne daya a garin Diguina dayan kuma a sansanin 'yan gudun hijira na Kolofata inda wata mata daure da jigidar bam ta yi kokarin kutsa kai a sansanin kafin jami'an tsaro su yi maganin ta.