1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin Boko Haram ya kashe sojojin Kamaru

July 25, 2021

Wani sabon hari da 'yan boko Haram suka kai a arewacin Kamaru, ya yi sanadiyyar rayukan dakaru da ma jikkatar wasu da dama. Hukumomi sun tabbatar da hakan.

https://p.dw.com/p/3y0hK
Kamerun Symbolbild Soldaten im Norden ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Rahotannin da ke fitowa daga Kamaru, na cewa wani harin mayakan Boko Haram ya salwantar da sojojin kasar akalla shida a ranar Asabar.

Maharan sun kuma jikkata karin wasu sojojin Kamaru da dama tare da yin awon gaba da makamansu.

Gwamnan yankin arewa mai nisa inda lamarin ya faru, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ta kafar watsa labarun cikin gida.

Hukumomin na Kamaru, sun yi bakin cikin rashin zaratan mayakan kasar a harin na Boko Haram a yankin Fotokol iyaka da Najeriya

Sun kuma jinjina wa sadaukar da rayuwarsu da sojojin suka yi saboda kasa.

Wani rahoton da 'yan sanda suka fitar, ya yi nunin cewa dakarun na Kamaru takwas ne suka mutu a harin, kamar yadda wasu majiyoyi ma suka tabbatar.