Hari ya kashe mutane 10 a Nijar | Labarai | DW | 27.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya kashe mutane 10 a Nijar

Mata 'yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 10 a wani harin kunar wake da suka kai a wani gari da ke Nijar

Wasu 'yan kunar bakin wake mata da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram sun kai tagwayen hare hare inda suka kashe mutane 10 a yankin gabashin Janhuriyar Nijar.

Hakimin garin N'Guigmi, Abba Kaya Issa ya fadawa kamfanin dillancin labaru na faransa na AFP cewar, mata biyu ne suka tayar da jigidar boma bomai da ke jikinsu, kana wani ya bude wuta akan fararen hula.

Matan da suka kai harin na cikin mutane 10 da suka mutu.