1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan na'urorin kwanfutar Bundestag

Usman Shehu UsmanJune 11, 2015

Bayan bincike na tsawon watanni yanzu ya tabbata cewa an yi kutse mai tsanani cikin na'urorin 'yan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag.

https://p.dw.com/p/1Ffo6
Cyber Angriff Symbol
Hoto: picture-alliance/dpa

A Jamus tun watanni aka fara binciken batun satar bayanai a na'urorin kwamfutar 'yan majalisar dokoki, yanzu bayan zurfin bincike an tabbatar da cewa akwai kutsen da ake yi cikin na'urorin da 'yan majalisar ke amfani da su. Sai dai yanzu zai kasance jan aiki na sake daukacin na'urorin 'yan majalisar ta Bundestag.

Kawo yanzu dai babu tabbacin ko daga ina ne ake kutsen ana satar bayanan 'yan majalisar. Sai dai bincike ya tabbatar hakan na faruwa, abinda kuma ya jawo babbar muhawara a majalisar dokokin. Domin kuwa in za a sake na'urorin sai an sauya kwamitoci sama da dubu 20, abinda kuma zai lakume miliyoyin Euro.

Masu kuste sun yi babban ta'adi

Hakan dai na nufin masu kutse na iya shiga daukacin na'urorin da 'yan majalisar ke amfani da su, kamar yadda Dennis Schirrmacher kwararre a harkar kwafuta ya bayyana.

"Suna iya daukar bayanai, suna kuma iya lalata ajiyar da aka yi. Suna ma iya sa makulli cikin na'urar yadda mai ita ba zai ai iya shiga ba, domin sai da makulli za a iya shiga."

A cewar masanan harkar na'urori da ke majalisar dokokin Jamus, har yanzu masu kutsen ba su daina shiga kwamfutocin wakilan majalisar ba. Hakan kuma na nufin ba a iya sanin iya nisan da suka yi wa majalisar ta Bundestag kutse ba.

Konstantin von Notz na jam'iyyar The Greens
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Fischer

Hakan ya zama wajibi kawai a maye gurbin kwamfutocin da wasu sabbi, domin haka ne kawai za a iya tabbatar an magance masu kutsen. Hakan kuwa na nufin sayo sabbin kwamfutoci sama da dubu 20.000, abinda zai ci miliyoyn kudin Euro kana kuma aikin da zai dau watanni kafin a kammala shi. Konstantin Notz dan majalisar Bundestag ne daga jam'iyyar The Greens.

"Abun dubawa shi ne ko ya kamata ra aba hanyar sadawar na'urori tsakanin majalisar dokoki da ta zartaswa. Domin muna bukatar tsarin sadarwarmu mai zaman kansa da bai hada da na ministoci ba. Domin bin didddigin ainihin ababen da wannan kutsen ya lalata."

Yanzu ayar tambaya da ta saura ita ce, tsawon lokaci da za a dauka domin shawo kan lamarin wato sake kwamfutocin 'yan majalisar. Kuma wane irin jinkiri zai kawo ma aikin 'yan majalisar? Kana kafin a kammala sauya na'urorin wadannen irin bayanai za su iya shiga hannun masu kutse a na'urorin majalisar dokokin ta Jamus?

Gagarumin aikin sake na'urorin Bundestag

Sandro Gaycken masanin fasahar zamani ne a cibiyar koyar da fasahar zamani ta Turai da ke Berlin, ya kuma bayyana yadda aikin sake gano wasu bayanan da aka lalata zai gudana.


"Da farko dai mutum zai tura bayanan a wata hanyar da aka yarda da ita, sannan za a sake shigar da wasu sabbin manhajoji cikin kwamfutocin da lamarin ya shafa, inda manhajar za ta leka don gano bayanan da aka fitar cikin kwamfutar domin dawo da su cikin kwamfutar ta aihini inda suke."

Bundestag Gedenkstunde zum Ende des Zweiten Weltkriegs
Zaman zauren majalisar dokoki ta BundestagHoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

Wata sarkakiya da za ta kawo cikas ita ce, 'yan majalisar dokokin na Jamus suna masu cewa, tamkar dai za a yi musu tsirara idan har sai sun mika dukkan kwamfutocinsu ga wasu masana na kasar Jamus. Yayin da a gefe guda ake cewa, in ma ba su bai wa masana na na'urori a Jamus don duba cikin kwamfutocin bisa yin gyara ba, ai tuni wasu batagari daga wajen kasar suke da daukacin sirrin da 'yan majalisar suka boye. Don haka hana wa masanan cikin gida ba zai taimaka wajen rufe asirin 'yan majalisar ba.

Tun a watan Junairun bana ma dai wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi kutse cikin shafin yanar gizo gwamnatin Jamus ciki har da na shugabar gwamnati Angela Merkel, inda suka bukaci Jamus ta daina goyon bayan Ukraine. Hakan kuwa ya faru ne 'yan kwanaki gabanin ganawar gwamnatocin kasashen biyu.