Hama Amadou ya tafi Faransa neman magani | Labarai | DW | 17.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hama Amadou ya tafi Faransa neman magani

Yayin da ake daf da zuwa zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Nijar, an kwantar da dantakarar na gamayyar 'yan adawa ta COPA wani asibitin birnin Paris na Faransa.

Hama Amadou

Hama Amadou na jam'iyyar Moden FA Lumana Afrika

Da Yammacin ranar Laraba ne dai (16.03.2016) wani jirgi na musamman ya dauki Malam Hama Amadou dan takara a zaben shugaban kasar Jamhuriyar Nijar zagaye na biyu, ya zuwa kasar Faransa domin yi masa magani. Hakan dai ya biyo bayan tabarbarewar yanayin lafiyarsa yayin da yake tsare a gidan kason garin Fillingue tsawon watanni hudu.

Tuni dai ofishin harkokin wajan kasar ta Faransa ya tabbatar cewa, bisa tambayar da Hama Amadou ya yi, Faransa ta amince da karbarsa domin yi masa magani, kuma mataki ne na imani.

A ranar Lahadin nan ce dai mai zuwa 'yan kasar ta Nijar za su koma ga zagaye na biyu na zaben tsakanin Shugaba Issoufou Mahamadou mai neman wa'adi na biyu da Hama Amadou. Sai dai a labarin baya-bayannan na cewa 'yan adawan na Nijar na wata ganawa a wannan Alhamis din domin fitar da matsayinsu na karshe dangane da zaben.