Hadari ne shan Chloroquine saboda corona | Labarai | DW | 23.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadari ne shan Chloroquine saboda corona

Masana harkokin lafiya a duniya, na ci gaba da gargadi kan hanzarin amfani da maganin nan na zazzabin cizon sauro wato hydroxychloroquine domin samun waraka daga COVID-19.

Gargadin dai na zuwa ne bayan samun wasu matsaloli na lafiya musamman ma masu nasaba da zuciya da aka gani tare da wasu majinyata kimanin dubu 100 da suka yi amfani da kwayar maganin a duniya.

Duniya dai ta raja'a ne kan wannan magani na hydroxychloroquine da nufin magnta corona, bayan tabbacin da shugaban Amirka Donald Trump ya bayar cewar yana iya warkar da cutar, koda yake masana sun karyata.

A Najeriya ma dai gwamnan jihar Bauchi, Malam Bala Muhammad, ya ce maganin ya taimaka masa wajen samun saukin cutar a lokacin da ya kamu da ita.

Hukumomin Najeriya inda sama da mutum dubu bakwai ke dauke da COVID-19, na gargadi kan yadda mutane ke ribibin sayen maganin, wanda ta ce ba ta bayar da lasisin yin hakan ba.

Ministoci 10 sun kamu da cutar a Sudan ta Kudu, amma gwamnati na musanta cewa Shugaba Salva Kiir ya kamu, bayan mataimakinsa Riek Machar ya tabbatar yana dauke da ita. 

Annobar dai na ci gaba da yaduwa a duniya, inda a yanzu ta fi karfi a yankin Latin Amirka.