Gwamnatin Jamus za ta taimaka a yaki Ebola | Labarai | DW | 05.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Jamus za ta taimaka a yaki Ebola

Gwamnatin Jamus ta ce za ta bayar da tallafi ga gwamnatin jamhuriyyar Kwango don yaki da annobar cutar Ebola da ke ci gaba da zama barazana ga rayukan al'umma.

Gwamnatin Jamus ta ce za ta duba yiyuwar tallafawa jamhuriyyar Kwango, a yakin da take da cutar Ebola ne a yayin da Ministan harkokin wajen kasar Heiko Maas ya kai wata ziyara a yankin Goma. Mista Maas ya ce,  bai dace a ci gaba da zura ido ana kallo, ba tare da an dauki matakin taimaka ma kasar, don ganin ta shawo kan cutar da ke ci gaba da zama barazana ga rayuwar al'umma ba.

A wani lokaci a wannan Alhamis, ministan zai gana da Shugaban kasar Felix Tshisekedi a Kinshasa babban birnin kasar, inda za su tattauna batun karin tallafin. A baya can, Jamus ta tallafawa kasar da kudi fiye da dala miliyan hudu, a lokacin da aka ayyana dokar ta bacci kan cutar mai saurin kisa.