Guguwar Eleanor ta yi barna aTurai
January 3, 2018Mahaukaciyar guguwa da ke tafiyar kilomita 160 cikin sa'a guda hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ta afkawa yammacin Turai a yau laraba, inda ta kada bishiyoyi da kau da jiragen kasa daga layin dogo da kuma kawo tsaiko wajan tashin jiragen sama.
Hukumomi sun bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da kimanin mutum biyar suka jikkata a kasashen Faransa da Suwizilan.
Bayaga tunkude jiragen kasa daga kan layin dogo, a kasashen Jamus da Suwizilan guguwar ta kuma katse wutar lantarki a yankuna da dama a kasashen Faransa, Birtaniya, Irelan da kuma suwizilan.
A Jamus an rufe wani bangare na manyan hanyoyin mota dake biranen Duisburg da Jülich da ke yammaci sakamokon bishiyoyi da suka fadi da kuma ambaliyar ruwa sakamakon mahaukaciyar guguwar.