1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke masu safarar mutane a Girka

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2022

Wasu Turkawa hudu sun shiga hannun mahukuntan kasar Girka, sakamakon zarginsu da safarar bakin haure zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/4L470
Girka, Kythira | Aikin ceto | Kwale-kwale | Bakin Haure
Kwararar bakin haure zuwa Turai, ba bakon abu ba neHoto: Ippolytos Prekas/kythera.news/AP/picture alliance

Matakin na zuwa ne, bayan samun wani kwale-kwale makare da bakin haure kusan 100 da ya samu matsala a wani tsibiri da ke kusa da birnin Athens. Jami'an tsaron gabar teku, sun sanar da cewa mutanen hudu na cikin bakin hauren kusan 97 da aka samu cikin jirgin ruwan a Arewa maso Gabasahin Tsibirin Kea da ke yankin Kudu maso Arewacin gabar ruwan birnin Athens fadar gwamnatin kasar Girka.