Girka ta gabatar da shirin neman tallafi | Labarai | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta gabatar da shirin neman tallafi

Girka na neman kasashen na Turai su bata adadin kudi da ya haure miliyan dubu 53 na Euro a matsayin sabon bashi.

Alexis Tsipras EU-Parlament

Alexis Tsipras na Girka

Gwamnatin kasar Girka ta gabatar da sabon shirinta na neman karin tallafin bashi kafin ta karasa durkushewa a fannin tattalin arziki.

Mahukuntan na birnin Athens sun gabatar da bukatar neman bashi ga kasashen na Turai na adadin kudi da ya haure miliyan dubu 53 na Euro.

Cikin bukatar da aka gabatar da ta hadar da sauye-sauye kan harkokin 'yan fansho da haraji a kan kayan siye da sayarwa, na zama mataki na karshe da ya ragewa kasar ta Girka kafin ta kammala durkushewa a fanninta na tattalin arziki koma ta fice daga kungiyar kasashe da ke amfani da kudin bai daya na Euro.

Mai magana da yawun Jeroen Dijsselbloem da ke jagorantar tawagar ministocin kudi daga kasashen na Turai ya tabbatar da cewa sun karbi bukatar da mahukuntan na Girka suka gabatar kuma a cewarsa abu ne mai kyau da zasu yi nazari a kansa.

A gobe Asabar ne dai ministocin za su zauna kan wannan bukata kafin taron koli da zasu yi a ranar Lahadi, inda shugabannin kasashen na EU za su yanke matsaya ta karshe kan rikicin bashin na Girka.