Girka: Jamus ta amince da tallafin ceto | Labarai | DW | 19.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka: Jamus ta amince da tallafin ceto

Majalisar dokokin tarayyar Jamus ta kada kuri'ar amincewa da tallafin ceto tattalin arziki kashi na uku da aka baiwa kasar Girka wadda tattalin arzikinta ke tanga-tangal.

EU Gipfel zu Griechenland in Brüssel

Firaministan Girka Alexis Tsipras da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugaban Majalisar dokokin ta Bundestag Norbert Lammert ya ce daga cikin 'yan majalisa 585, mutum 454 sun amince da wannan kuduri, 113 sun kada kuri'ar rashin amincewa yayin da mutum 18 suka yi rowar kuri'unsu.

Ministan kudin Jamus kana mamba na majalisar ta Bundestag Wolfgang Schaeuble ya ce da tallafin takwarorinta na kungiyar kasashen Turai da ke amfani da takardar kudin euro, Girka ta sake samun damar da za ta iya amfani da ita wajen ceto tattalin arzikinta.