1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka: An gano mutane 41 a motar dakon kaya mai firji

Binta Aliyu Zurmi
November 4, 2019

A Kasar Girka, an gano wasu mutane 41 da aka boye a wata motar dakon kaya. Akasarinsu dai sun fito ne daga kasar Afganistan kamar yadda 'yan sandan da suka gano motar suka sanar.

https://p.dw.com/p/3SSCO
Griechenland Migranten aus Kühllaster befreit
Hoto: Reuters/S. Karipidis

Rahotannin sun nuna cewa mutanen dukkansu na raye kuma na'urar firjin motar da suke cikinta, ba a kunne take ba. 

Da safiyar yau ne 'yan sandan suka tsayar da motar domin bincike kan hanya, inda daga bisani suka gano mutanen. 

Tuni dai aka kama direban motar da ma sauran mutanen. Tun a shekarar 2015 Girkar ke fama da dubban 'yan gudun hijira da suka ketaro daga Turkiyya a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Ko a karshen watan jiya ma an kama wata mota a Birtaniya dauke da gawarwakin mutane 39 cikin irin wannan doguwar mota mai firji.