Gidauniyar Jamus ta karrama matan Kamaru
June 6, 2023Talla
Matan da suka samu wannan nasara, na daga cikin matan da ke fadi tashin ganin an zauna lafiya a Kamarun.
Gidauniyar Jamus da takarrama matan su 32, ta kwashe shekaru 45 tana wannan aiki da zimmar kyautata dangantaka tsakanin Jamus da kasashen nahiyar Afirka.
Yankunan kasar Kamaru 10 dai na fama da matsalolin tsaro, inda galibi mata ne suka fi fama da wahalhalun da rashin kwanciyar hankalin ke haifarwa.
Dukkanin matan da suka yi wannan nasarar dai sun nuna farin cikinsu, musamman ganin irin gwagwarmayar da suke sha a kungiyance wajen ganin an samu zaman lafiya a kasar.