Ghana: Hijirar matasa zuwa kasashen waje | Zamantakewa | DW | 19.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ghana: Hijirar matasa zuwa kasashen waje

Ghana na a jerin kasashen Afirka da ke a sahun gaba wajen fitar matasansu zuwa kasashen waje musamman Turai da Amirka ko Saudiyya da kwadayin samun ingantacciyar rayuwa.

Batun hijira zuwa turai dai, daddaden batu ne wanda ya zamo ruwan dare gama duniya. A shekarun baya akasarin 'yan gudun hijirar Afirka zuwa Turai na fitowa ne daga kasashen Larabawa na Arewacin Afirka musamman kasashen Maroko, Aljeriya da Tunusiya. Sai dai kuma sannu a hankali lamarin ya yadu zuwa kasashen Afirka bakar fata. Kasar Ghana na daga cikin kasashen na Afirka da a yanzu akasarin matasa ke yin irin wadan nan tafiye-tafiye a bisa dalilan da suke dangantawa da matsin tattalin arziki. 
 

A ko wace shekara ta Allah daruruwan 'yan kasar Ghana ne musamman matasa ke bin sahun takwarorinsu na kasashen Afirka da dama wajen yin kasadar rayukansu a cikin Hamada da tekun Baharum, da zummar shiga nahiyar Turai da kwadayin samun kyakyawar rayuwa. A lokuta da dama dai, tafiya ce da ake wa hangen dala, wacce a karshe kuma dai ake kammala ta a tutar babu inda ake kwasu wasunsu zuwa gida. A ranar 23 ga watan Nuwamba, 2016, gwamnatin Amirka ta maido da 'yan Ghana 108 gida. Wannan mutun na daga cikin jerin 'yan kasar Ghanar da Amirka ta maido kasarsu a shekarar ta bana ya kuma shaidawa DW yadda suka tsinci kansu a hanyar hijirar.

"Da farko na tafi Brazil ne, daga can na isa Ekwado sannan na wuce Kwalambiya na ratsa Panama da Nikaraguwa. Daga nan na shiga Unduras na wuce Mexiko. Daga nan muka sake komowa Panama inda muka yi tafiyar kwanaki biyar cikin daji inda wani daga cikin abokan tafiyar tamu ya rasu kafin mu shiga kasar Amirka. Wasu daga cikin abokanin tafiyarmu na baya jirgin ruwansu ya kife da su wajen 30 da wani abu suka rasu"

Wani malamai mai suna Alhaji Awe boy na shima daga cikin wadanda aka maido gida daga kasar Saudiyya inda ya yi zaman gudun hijira, ya kuma yi wa wakiliyar DW a Ghana jamila Ibrahim Maizango karin bayani yana mai cewa:

 

"Na yi tafiya zuwa Saudiyya inda na yi aiki shekaru 11. Zaman da muka yi a can ba mu da takarda, kullum muna guje-guje da boye-boye"

Sai dai da dama ne ke sha da kyar a wannan hijirar. Malam Gariba ya shaida wa wakiliyar ta DW a birnin Accra dalilan da suka tursasa shi fita daga gida.

" Ni na yi tafiya ne da kudi zuwa kasar Malesiya. Amma an kama ni a can aka tsare ni wata daya gidan kaso. Bayan an sake ni sai na ga duk kudin da na mallaka na rasa shi. Na yi tunanin in na dawo Ghana yaushe za ni iya samun wannan kudi. Shi ya sa na kama hanyar zuwa Libiya. Wannan tafiya akwai hadari a cikinta. Domin ana tsuba mutane da dama a saman wata karamar mota. Bayan mu isa a Libiya an kama mu a sayar wa Larabawa. Kuma in ka yi turjiya sai a kashe ka. A gabana an kashe mutun akalla ukku. Ni kaina an harbe ni, yanzu haka akwai bindiga a kafata" 

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa a shekara ta 2015 adadin bakin haure ya kai mutun miliyan 244.

Sauti da bidiyo akan labarin