Gaskiya ta yi halinta kan sanya kwaya cikin kayan matafiya a Kano | Siyasa | DW | 30.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gaskiya ta yi halinta kan sanya kwaya cikin kayan matafiya a Kano

Hukumomi a kasar Saudiyya sun saki Zainab Aliyu da aka sanya wa kwaya a kayanta a filin jirgin saman Malam Aminu Kano yayin tafiyarta Umrah.

Tun gabanin samun labarin sakin Zainab Habibu Aliyu a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, dalibai a Kano sun gudanar da zanga-zangar neman a sake ta. Ita dai Zainab Aliyu daliba ce da aka sanya wa kwaya cikin kayanta a filin jirgin saman Malam Aminu Kano yayin tafiyarta aikin Umrah a kasar Saudiyya wasu watanni da suka gabata. Bayan bincike na tsawon lokaci an gano cewa wasu ma'aikata ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke a birnin Kano suka auna wata jakka da sunanta wadda kuma suka sanya kaya a cikinta.

Malam Mohammed Ajiya mataimakin kwamandan hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a filin jirgin saman na Kano ya yi karin haske yana mai cewa binciken da suka yi a Najeriya sun kame mutane shida da suke aiki a bangarori dabam-dabam a filin jirgin saman na Kano.

Shi ma a hira da DW ta yi da shi mahaifin yarinyar, Habibu Nuhu ya tabbara wa tashar DW sakin 'yar tasa. Ya ce wadanda aka kame a Najeriya da sanya kwaya cki kyan 'yarsa tuni sun amsa laifin aikata wannan makirci.

Sauti da bidiyo akan labarin