Ganawar Merkel da Karzai a Berlin | Labarai | DW | 19.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Merkel da Karzai a Berlin

Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ta bayyana cewa manufar gwamnatinta na samarda da tallafin sojoji da jamian farara hula wa kasar Afganistan,na kann hanya madaidaiciya.Tayi wannan furucin ne bayan ganawarta da shugaba Hamid Kharzai a birnin Berlin,a rangadin aiki dayake yi anan jamus.a nashi bangaren ,shugaban na kasar Afganistan yayi maraba da zartarwar da jamus tayi na tura jiragen saman sintiri kirar kamfanin Tornado zuwa yankin kudancin kasar .Shugaba Karzai a wannan ganawa tasu da Merkel ya jaddada bukatar a dada bawa kasarsa tallafi,a bangaren kasashen turai.