Ganawa kan zaman lafiyar Libiya a kasar Jamus | Labarai | DW | 10.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawa kan zaman lafiyar Libiya a kasar Jamus

Wakilan majalisar dokokin kasar Libiya suna kasar Jamus domin tattaunawa da kasashen Kasashen Turai bisa hanyoyin da za a samar da zaman lafiya a kasar

Wakilan majalisar dokokin kasar Libiya suna kasar Jamus domin tattauna hanyoyin da za a samar da zaman lafiya a kasar da ke yankin arewacin Afirka. Ana sa ran haka zai taimaka wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa da zai kawo karshen kokuwar neman madafun iko.

Mataimakain shugaban majalisar dokokin kasar Emhemed Shoaib da mai Magana da yawun majalisar dinkin duniya duk sun tabbara da labarin, duk da yake akwai yuwuwar sabani kan hanyar samar da zaman lafiyar. Mai shiga tsakani kann rikicin kasar ta Libiya na MDD, Bernardino Leon ya mika wa bangorirn shirin hanyar samar da zaman lafiya lokacin tattaunawa a kasar Moroko.

Sai dai rarrabuwar karamin abu ne idan aka kwatanta da jan aikin da ke gaban Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin bangarorin sun amince da shirin na zaman lafiya.