1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen G20 za su yi mahawara kan corona

Zainab Mohammed Abubakar
November 21, 2020

Wakilan kasashe masu cigaban masana'antu na G20, na shirin tabka mahawara kan annobar corona da kuma hanyar da za a dosa da zarar an cimma nasarar shawo kan cutar.

https://p.dw.com/p/3ldts
Saudi-Arabien Riad vor dem G20 Gipfel
Hoto: Fayez Nureldine/AFP/Getty Images

A wani mataki kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana game da yiwuwar barkewar wata annoba nan gaba, Kungiyar Tarayyar Turai EU na shirin gabatar da yarjejeniya kan cuta mkamanciyar corona da ka iya yaduwa a duniya.

Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya ce, yarjejeniyar kasa da kasa za ta taimaka wajen martanin gaggawa da hadin kai ta hanyar da ta dace, da zarar irin wannan yanayi ya auku.

Tuni dai Asusun bada lamuni na duniya ya ayyana cewar, farfadowa daga annobar corona ba zai zama abu mai sauki ba, kuma za ta bar mummunan tabo a tattalance.