Ficewar Birtaniya daga EU zai janyo karin haraji ga ′yan kasar | Labarai | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ficewar Birtaniya daga EU zai janyo karin haraji ga 'yan kasar

Sakataren kudin Birtaniya ya yi gargadi game da karin haraji idan kasar ta fice daga kungiyar EU a kuri'ar raba gardama ta ranar 23 ga watan Yuni.

Großbritannien Schatzkanzler George Osborne Herbstansprache

George Osborne lokacin wani jawabi a gaban majalisar dokoki da ke birnin London

Sakataren kudin Birtaniya George Osborne ya ce 'yan Birtaniya ka iya fuskantar karin kudaden haraji idan kasar ta kada kuri'ar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai EU. Ya ce matakin ficewar zai yi illa ga harkokin zuba jari da tattalin arziki da kuma zamatakewar iyali a kasar. A lokacin da yake magana a birnin London Sakatare Osborne ya ce dole ne a kara kudin haraji kuma gwamnati za ta rage yawan kudaden da take kashewa idan Birtaniyar ta fita daga Tarayyar Turai. Sakataren kudin ya ce dole kasar ta samar da wani kasafin kudi na gaggawa da zai tanadi tsuke bakin aljihu, matukar 'yan kasar suka kada kuri'ar amincewa da yin bankwana da kungiyar EU a kuri'ar raba gardama da za su kada a ranar 23 ga watan nan na Yuni. Binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar bayan nan ya nuna yawan masu goyon bayan a fita daga EU na karuwa.