1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan samun kyautatuwar rayuwa na dusashewa a Girka

Wolfgang Landmesser/ Mohammad Nasiru Awal January 25, 2016

Shekara guda da mulkin gwamnatin jam'iyyar Syriza a Girka, har yanzu al'ummar kasar na cikin kuncin rayuwa da rashin aikin yi ga kuma karancin kudi a hannun jama'a.

https://p.dw.com/p/1HjZB
Griechenland Alexis Tsipras
Hoto: Getty Images/AFP/A. Tzortzinis

A lokacin da ya dare kan kujerar mulki shekara guda da ta gabata, Firaministan Girka Alexis Tsipras ya kasance wani ja gaba a tsakanin masu ra'ayin sauyi a Turai. Duk da cewa an dakatar da barazanar talaucewa da Girkar ta fuskanta watanni 12 da suka wuce, amma har yanzu ba a kawar da wannan barazana gaba daya ba, yayin da kuma matsalar kwararowar 'yan gudun hijira ta kara jefa kasar cikin halin rashin tabbas.

A wata kasuwa da ke Athens babban birnin kasar Girka jama'a na nuna rashin jin dadinsu. Ko shin an ga sauyi tun bayan da gwamnati karkashin jam'iyyar Syriza ta hau kan mulki a bara? Parakletos wani mawaki ne da ke kusa ya ce gaskiya ba abin da ya canja.

"Shin yaya halin rayuwar mutumin da ya kwashe tsawon shekaru uku ba ya aiki zai kasance? Muna cikin mawuyacin hali. 'Yan siyasa suna yaudararmu. Ga misali sun kirkiro da harajin nuna zumunta, amma marasa aikin yi ba sa samun komai daga ciki."

Harkokin ciniki sun yi rauni saboda talauci

Shi kuwa Phillippos Philippakis da tun shekaru 40 ke nan yake aiki a kasuwar kifi, ya ce kullum cinikin yana ja da baya ne. Kuma ba abin da ya canja, in banda talauci da ke karuwa a kullum.

Griechenland Geldautomat außer Betrieb
Hatta injunan cire kudi na ATM ba sa aikiHoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

Sai dai Philippakis bai dora laifin kan gwamnatin Firaminista Alexis Tsipras ba, wanda ya ce shi kadai ba zai iya tinkarar sauran kasashen Turai ba.

"Yana fuskantar kasashen Turai da ke gaba da mu. Burinsu shi ne su ga gazawar Tsipras. Ba sa son gwamnatin masu ra'ayin sauyi ta samu nasara. A gare ni hanya daya tilo da za mu magance wannan matsala ita ce Girka ta fice daga tarayyar Turai da jerin kasashe masu amfani da takardun kudin Euro."

A tsakiyar shekarar 2015 kiris ya rage Girka ta fice daga jerin kasashe masu cin kudin Euro, amma aka samu masalaha bayan da Tsipras ya amince da sabon shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.

Al'umma ta fusata saboda rashin ganin wani sauyi

Sai dai shekara guda bayan nasarar lashe zabe, jagoran na jam'iyyar Syriza na fuskantar fushin al'ummarsa. Akasarin wadanda suka jefa masa kuri'a yanzu suna gudanar da zanga-zanga a kan tituna.

Griechenland Proteste gegen die geplante Rentenreform
Zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihuHoto: Reuters/A. Konstantinidis

Dubban lauyoyi da likitoci da injiniyoyi sun shiga cikin boren da ake wa Firaministan, domin sun shiga halin ni 'ya su, inji wannan injiniya.

"Ina da ofishin aikin injiniya, mata ta lauya ce. Ke nan matsalar ta shafe mu gaba daya. Shirin kara mana haraji na zama wani gurgun mataki da zai durkusar da mu baki daya."

Idan aka fara aiwatar da sabbin sauye-sauyen, gwamnatin kasar ta Girka za ta zaftare fiye da kashi 50 cikin 100 na albashin kwararrun ma'aikata masu zaman kansu wato kamar injiniyoyi da lauyoyi da dai sauransu.

Shekara guda bayan gagarumar nasarar da Tsipras ya samu, fata na kara gushewa, domin kawo yanzu ba a hango wani haske ba. Duk da cewa a bara tattalin arzikin kasar bai yi rauni kamar yadda aka yi farbaga ba, amma sai fa kamfanoni sun fara zuba jari sannan za a iya kirkiro da sabbin guraben aiki, a lokacin ne kuma Girka za ta fara ganin alamun kyautatuwar al'amura.