Syriza jam'iyya ce da aka kafa a kasar Girka a shekara ta 2004. Ta lashe zaben gama gari da aka shirya a watan Janairun 2015.
Shugabanta shi ne Firaministan Girka Alexis Tsipras. Adawa da matakin tsuke bakin aljuhu da wannan jam'iyya ta sa gaba ya sa ta kai ruwa rana da Kungiyar Tarayyar Turai lokacin da Girka ta yi fama da matsin tattalin arziki.