Firaministan Girka ya yi marabus | Siyasa | DW | 21.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Firaministan Girka ya yi marabus

Babbar jam'iyyar adawa ƙasar ta New Democracy na sukar Alexis Tsipras kan murabus ɗin da ya yi.

Griechenland Alexis Tsipras Rücktritt

Alexis Tsipras

Firaministan ya baiyana matsayarsa na yin marabus a wani jawabin da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin ɗin ƙasar, inda ya ce gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen cimma yarjejeniyar ceto tattalin arzikin Girka. To amma wannan matsayin na Tsipras ya janwo zazzafar martani daga babbar jam'iyyar adawar ƙasar wato New Democracy, inda suka yi taron manema labari kan matsayarsu na kafa gwamnati kafin wa'adin da ƙasar za ta shiga zaɓuɓɓuka. Evangelos Meimarakis shi ne shugaban jam'iyyar ND wanda ya tabbatar da cewar jam'iyyarsu ta amince da a kafa sabuwar gwamnati sannan sun bayyana shirinsu shiga zaɓuɓɓukan ƙasar.

Martanin 'yan siyasa kan marabus ɗin na Alexis Tsipras a Girka

"Tilas na shaida muku cewar jam'iyyarmu ta kimtsa kuma da ma tun can ba mu amince da murabus ɗin Tsipras ba. A don haka hukumar zaɓe a shirye take ta sanar nan ba da jimawa ba. Ina da yaƙinin cewar shugabanni na ƙwarai na da nasara kan ko wani fafutuka."To amma Tsipras ya baiyana irin matsin lambar da ya fuskanta na zazzafar adawa a cikin jam'iyyarsa ta Syriza bayan da ya amince da ɗaukar tsauraran matakan tsuke bakin aljihu domin samun Euro milyan-dubu 86 cikin shekaru uku. Ya ce yanzu lokaci ne da 'yan ƙasar zasu yanke wa kansu hukunci kan cewar ko ya tallafa wa ƙasar dan ta farfaɗo. Tsipras ya yi waɗannan jawabai ne a ganawarsa da shugaban ƙasar Prakopis Pavlopouos.

"Banga alamar kafa gwamnatin haɗaka ba, a don haka tilas abi tsarin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a cikin manyan alƙalai 3 da ake da su don jagorantar ƙasar kafin zaɓe kamar yadda doka ta tsara."

Lamarin ya ɗauki hankalial al'ummar Girka a kan wannan batu na marabus

Wannan batu dai a yanzu ya ɗauke hankalin 'yan ƙasar Girkan da dama inda wasu ke maraba da wannan hukunci yayin da wasu kuwa ganin halin da ƙasar ke ciki ba ta cece kuce ba ne a yanzu.Dimitris Rapidis wani manazarcin lamuran siyasa ne a ƙasar Girka da ke ganin siyasa da tattalin arzikin ƙasar na cikin rudani.

"Akwai dalilai da dama da ya sa tsipras ya yanke wannan hukunci harya ya nemi da ayi zaɓe,na farko ya fuskanci adawar cikin gida na yunƙurin ƙirƙiro da sabuwar jam'iyya."

Ana sa ran ranar 20 ga watan gobe na Satumba za a shiga rumfunan zaɓe a ƙasar, domin zaɓen sabuwar gwamnati, kamar dai yadda jami'an gwamnatin suka nunar.

Sauti da bidiyo akan labarin