Majalisar dokokin Girka za ta kada kuri′a kan matakin na biyu na ceto tattalin arzikin kasar | Labarai | DW | 22.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Girka za ta kada kuri'a kan matakin na biyu na ceto tattalin arzikin kasar

Firaministan Girka zai sake dogara kan 'yan adawa kan kashi na biyu na shirin ceton tattalin arzikin kasar

A wannan Laraba majalisar dokokin kasar Girka za ta kada kuri'a kan amincewa da mataki na biyu na matakan tsuke bakin aljihu, wanda zai kai kasar ta fara samun makuden kudaden da take nema domin ceto tattalin arzikin kasar.

Haka ya zama gwaji ga Firaminista Alexis Tsipras wanda yake fuskantar tawaye daga wasu daga cikin mambobin jam'iyya mai mulki, tare da dogara a kan 'yan adawa domin samun nasara. A makon jiya wasu mambobin jam'iyyar Syriza mai mulki sun kada kuri'ar rashin amincewa da matakan sauye-sauye da sake fasalta tsarin fensho na kasar, abin da ya janyo aka yi gyaran fuska wa gwamnati.

Wannan matakin babu wata takkadama a kai saboda majalisar dokokin ta Girka za ta amince ne da matakin kasashen Turai bisa kare makuden kudaden masu ajiya a bankunan kasar ta Girka, da sauye-sauye a tsarin shari'ar kasar.