Alamun kafa gwamnati cikin gaggawa a Girka bayan nasarar da Syriza ta samu | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alamun kafa gwamnati cikin gaggawa a Girka bayan nasarar da Syriza ta samu

Shugabannin siyasa a Jamus sun ba da ra'ayoyi mabanbanta game da sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin Girka da jam'iyyar sauyi ta Syriza ta lashe.

Griechenland Alexis Tsipras mit Panos Kammenos Koalitionsgespräche

Shawarwarin kulla kawance: Alexis Tsipras da Panos Kammenos shugaban 'yan ra'ayin rikau

Bayan nasarar da jam'iyyar Syriza ta samu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar Girka, an fara ganin alamun kafa gwamnati cikin hanzari. Shugaban Syriza Alexis Tsipras ya sanar cewa zai sabunta kawance da jam'iyyar 'yan mazan jiya ta Anel. Su ma kasashen Turai sun yi kira da a gaggauta kafa gwamnati a kasar ta Girka. Shugabannin siyasa a Jamus sun mayar da martanin mabanbanta dangane da sakamakon zaben na Girka. Shugaban jam'iyyar sauyi ta Linke a Jamus Gregor Gysi ya yi farin ciki da sakamakon zaben da ya ce ya saba da ra'ayin kungiyar EU wadda ta so ta ga bayan gwamnatin masu ra'ayin sauyi. Ita kuwa jam'iyyar CDU a ta bakin mataimakiyar shugabarta Julia Klöckner fata ta yi cewa Firaminista Alexis Tsipras zai cika alkawarin da ya dauka na aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu.

"Na yi imani Tsipras bai da wani zabi face ya ci gaba da mutunta yarjeniyoyin da aka kulla da shi. Abin da muke sa rai ke nan."