1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsanancin zafi a kasashen Turai

Zulaiha Abubakar
June 25, 2019

Shugaba Emmanuel Macron ya bukaci al'umma su kasance cikin shiri bayan hukumar kula da yanayi ta tabbatar da karuwar zafi da maki 40 a ma'aunin Celsius a kasashen Beljiyam da Jamus da kuma Faransa a kwanaki masu zuwa.

https://p.dw.com/p/3L2Pt
Frankreich | Hitzewelle
Hoto: Getty Images/AFP/P. Huguen

Ya kuma kara da cewar a lokutta irin wannan mata masu ciki da jarirai da marassa lafiya da kuma masu shekaru sun fi kowa fuskantar kalubale, don haka ya zama wajibi kowa ya sanya ido a kansu don kai musu agajin gaggawa idan bukatar hakan ta taso. Tuni ministar lafiyar kasar Agnes Buzyn ta sanar da irin tanadin da ma'aikatar lafiya ta Faransa ta yi sakamakon yawaitar rasa rayukan da kan faru idan zafi ya tsananta. 

Anata bangaren hukumar yanayi ta Jamus ta sanar da cewar rabon da kasar ta fuskanci irin wannan yanayi tun 1947 ana sa ran yanayin zafin zai haura mataki na 40 a ma'aunin Celsius a tarayyar ta Jamus a gobe Laraba.