Shugabannin kasashen Tarayyar Turai 27 sun dauki alkawarin bai wa Turkiya taimako iya karfinsu don rage radadin bala'in girgizar kasa da ta auku a kasar da Siriya.
Shugabannnin Tarayyar Turai 27 suka rattaba hannu kan takardar wace suka aika wa shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, inda suka nuna masa matukar goyon bayansu a dai-dai lokacin da kasarsa ta shiga wani rikicin ba zata. Shugabannin na EU a taronsu na wannan Alhamis a birnin Brussel, sun kuma yi tsit na miniti guda don tunawa da 'yan Turkiya da da Siriya da suka mutu a girgizar kasar. Shugabannin sun ce taimakonsu ga 'yan Turkiya da Siriya, sai iya inda karfinsu ya tsaya. A daya bangaren taron na Brussel sun gayyaci shugaban kasar Ukraine a taron, wanda ya jaddada bukatarsa ta neman lallai sai kasashen Yamma su gaggauat aika wa kasarsa makamai yayinda yakinsu da Rasha ke kara daukar lokaci.