1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: EU ta umurci mambobinta su rage shan gas

July 20, 2022

Matakin na a matsayin 'kandagarki' ga yiwuwar katsewar makamashin da Turai ke tunanin Rasha za ta iya yi.

https://p.dw.com/p/4EQdO
Nordmazedonien Rede Ursula von der Leyen
Hoto: Arbnora Memeti/DW

Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta wallafa wasu dabaru na gaggawa da take sa ran tunkarar matsalar  karancin makamashi a kasashen kungiyar. Shugabar hukumar Ursula von der Leyen ta zargi Rasha da amfani da batun makamashin a matsayin sandar duka domin mayar da martani kan takunkuman da aka sanya mata biyo bayan mamayar da take yi wa Ukraine. 

Daga cikin dabarun da EU ta fitar, kungiyar, ta bukaci mambobinta su rage kaso 15 cikin 100 na makamashin iskar gas da suke amfani da shi a lokacin hunturu tsakanin watan Agusta zuwa Afrilu.