EU za ta kara wa Rasha takunkumi | Labarai | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta kara wa Rasha takunkumi

Za dai a cimma matsaya ta karshe kan wannan yarjejeniyar kara tsayin takunkumin kan Rashar nan ba da dadewa ba, wanda kuma za a wallafa a kan mujallar kungiyar ta EU.

Belgien EU Gipfel Gruppenbild

Mahalarta taron EU

Jakadu daga kungiyar hadin kan Turai ta EU sun cimma matsaya wacce za ta bada dama a kara tsawon wa'adi na takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Rasha da karin watanni shida anan gaba kamar yadda wani jami'in diplomasiya ya bayyana a ranar Juma'an nan bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba. Wannan dai na zuwa ne bayan tsaiko da aka samu a ci gaban yarjejeniyar tsagaita wuta a Gabashin Ukraine.

Daga nan zuwa ranar Talata ne dai za a cimma matsaya ta karshe kan wannan yarjejeniyar kara tsayin takunkumin kan Rashar, wanda kuma za a wallafa a kan mujallar kungiyar ta EU a cewar wannan jami'i. An dai kakaba wa kasar ta Rasha takunkumi na tattalin arziki tun a watan Yuli na shekarar 2014 saboda mamayarta a yankin Kiremiya da ma tsoma bakinta a rikicin Gabashin Ukraine.

Wannan takunkumi dai da kasashen na EU suka kakaba wa Rasha na sanyawa dukkanin bangarorin biyu na ji a jikinsu kan batun da ya shafi tattalin arziki.