1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Tsarin sauye-sauye na Shugaba Macron

Salissou Boukari
September 26, 2017

A wannan Talatar ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da tsarinsa na kawo sauye-sauyen da za su karfafa kungiyar Tarayyar Turai cikinsu har da batun harkokin tsaron Turai.

https://p.dw.com/p/2klcG
Frankreich Emmanuel Macron, Präsident | Präsentation Europäische Initiative in Paris
Shugaban kasar Faransa Emmanuel MacronHoto: Reuters/L. Marin

A cikin shawarwarin shugaban na Faransa ya nemi da a kikiro wani tsari na tsaro na bai daya na Tarayyar Turai, tare da samar da ma'aikatar kirkire-kirkire, da 'yan sanda na hadin gwiya masu tsaron iyakoki, da ma ma'aikatar shari'a ta Turai. A ckin jawabin da ya yi na fiye da awa daya a jami'ar Sorbone da ke birnin Paris, Shugaba Macron ya yi kira da a kafa wata rundunar sojoji ta gaggawa ta Tarayyar Turai daga nan zuwa 2020, tare da samar da kasafin kudi na tsaro na bai daya da kuma tsarin gudanar da ayyukan rundunar yadda za ta yi aikinta ba tare da bata lokaci ba da zarar wata matsala ta taso.