1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kara wa Ukraine miliyoyin kudi

July 12, 2022

Tarayyar Turai ta sake mika wa Ukraine wasu kudade da take ganin za ta iya amfani da su wajen kyautata al'amura a kasar saboda rigimar da ta samu kanta a ciki.

https://p.dw.com/p/4E1zA
Belgien EU Gipfel Ursula von der Leyen
Hoto: Geert Vanden Wijngaert/AP photo/picture alliance

Kungiyar Tarayyar Turai, ta amince da bai wa Ukraine kudaden da suka kai Euro biliyan guda, daidai lokacin da Rasha ke zafafa ke hare-hare a kan kasar.

Kudaden da Tarayyar Turan ke bai wa Ukraine a matsayin rance, kari ne a kan wasu Euro biliyan daya da miliyan 200 da suka bai wa kasar cikin watan Fabrairu.

Kungiyar ta EU na ganin kudaden za su taimaka wa Ukraine wajen amfani da su a muhimman bangarorin da ke fama da tarnaki sakamakon mamayar da Rasha ta kai mata.

Wannan na zuwa ne yayin da Amirka a nata bangaren, ke bai wa Ukraine din dala biliyan daya da dubu 300 a matsayin tallafi.

Sai dai ana kallon akwai sauran turanci a kan biliyoyin Euro da kasashen Turan suka shirya ba Ukraine a matsayin rance.