EU ta ce ba za ta juya baya ba ga masu neman mafaka | Labarai | DW | 31.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta ce ba za ta juya baya ba ga masu neman mafaka

Hedikwatar EU da ke a Brussels za ta kara bada miliyan biyar na Euro dan tallafa wa kasar ta Faransa cikin ayyukan jinkai da take yi na taimakon 'yan gudun hijira dubbai da ke a yankin na Calais.

Frankreich Manuel Valls in Calais mit Timmermans und Avramopoulos

Manuel Vallsministan harkokin cikin gidan Faransa a yankin Calais da Timmermans na EU da sauran jami'ai

Mataimakin shugaban hukumar Tarayyar Turai, Frans Timmermans ya bayyana cewa ba zasu taba juya baya ba ga duk wadanda ke neman tsira da rayukansu.

Timmermans ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara a gabar teku da ke Arewacin Faransa a yankin Calais a ranar Litinin din nan.

Ya kara da cewa hukumar tasu da ke da hedikwata a Brussels za ta kara bada miliyan biyar na Euro dan tallafa wa kasar ta Faransa cikin ayyukan jinkai da take yi dan taimakon 'yan gudun hijira dubbai da ke a yankin na Calais a bisa muradinsu na danganawa da kasar Birtaniya.Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta ce babu batun tsaurara dokoki a lamuran da suka shafi 'yan gudun hijira.