EU da Amirka sun kakaba wa Rasha takunkumi | Siyasa | DW | 17.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU da Amirka sun kakaba wa Rasha takunkumi

Kungiyar EU da Amurka sun kakabawa Rasha takunkumi da suka danganci hana taba kudi ko kadara da ma na tafiye-tafiya sakamakon dambawar siyasarsu da Ukraine.

Russland Präsident Wladimir Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Sakamakon zaben kuri'ar raba gardaman da al'ummar Kirimiya suka kada ta ballewa daga Ukraine ne dai ya sanya kasashen na EU da ma Amurka yanke shawarar kakabawa Rasha jerin takunkumi a wani mataki na nuna fushinsu game da irin rawar da Rashan ke takawa dangane da rikicin siyasar Ukraine.

A wani taro da ministocin harkokin wajen kungiyar ta EU gami da wasu jiga-jiganta suka yi yau dai sun ce daukar wannan mataki ya zama dole, duba da irin kokarin da aka yi na gujewa kawowa ga wannan hali da ake ciki na ballewar Kirimiya daga Ukraine.

ashton, catherine, eu, außenbeauftragte

Catherine Ashton ta ce EU ta dauki matakin sanya takunkumi don an gaza samun daidaito

Da take bayani game da wannan takunkumi da EU ta kakabawa Rasha kantomar da ke kula da manufofin ketare ta kungiyar EU Catherine Ashton ce ta yi ''sakamakon gaza samun wani cigaba mai ma'ana mun yanke shawarar daukar karin matakai kan Rasha musamman ma kan mutanen da ke da hannu wajen yin katsalandan ko kuma barazana ga 'yan cin gashin kan da Ukraine take da shi a matsayin kasa.''

Mutane da wannan takunkumi ya shafa dai sha uku daga ciki na hannun daman shugaban Rasha Vladmir Putin ne yayin da takwas daga cikinsu ke zaman 'yan kasar Ukraine, ciki kuwa har da hambararren shugaban kasar Victor Yanukovic da wasu mukarrabansa wadanda kanwasu ba ta jikuwa da sabbin mahukuntan kasar Ukraine din na yanzu.

EU dai ta ce za ta hana wadannan mutane ashirin da daya shiga kasashen da ke cikin kungiyar da ma hana su taba kudade ko kadarorin da suke da suka mallaka a kasashen waje.

Obama Rede zur Ukraine 17.03.2014

Amurka ma ta bi sahun EU wajen daukar tsattsauran mataki kan Rasha

Ita ma dai Amurka wadda ke kan gaba a jerin kasashen yamma da adawa da matsayin Rasha a rikicin siyasar ta ce ta dau kwatankwacin matakan da EU ta dauka kan wadannan mutane.

Tarayyar Jamus wadda kamar takwarorinta ke nuna rashin amincewarta da ballewar yankin na Kirimiya daga kasar Ukraine, kira ta yi ga mahukuntan Moscow da su kauracewa keta alfarmar Ukraine kasancewar ita ma kasa ce da ke da 'yanci kamar kowacce kasa, kamar dai yadda kakakin shugabar gwamnatin Jamus kenan Steffen Seibert ke cewa:

''Ya kamata Rasha ta dakatar da kokarinta na yin karen taye ga 'yancin cin gashin kan Ukraine da ma dagula lamura a kasar. Kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus ta bayyana a makon da ya gabata, Rasha ta nuna cewar ba abokiyar samar da zaman lafiya ba ce don ta na amfani da raunin da makotanta ke da shi wajen cimma wasu buruka na ta.''

Merkel Rede in Dublin 07.03.2014

Jamus na fatan Rasha za ta kauracewa yin katsalanda a Ukraine

To yayin da kasashen Turai da na yammacin duniya ke daukar tsauraran matakai kan Rasha, ita kuwa gwamnatin Rashan a nata hannu hali ta nuna na ko in kula dangane da wannan matsayi da EU da Amurka suka dauka a kanta, har ma mataimakin Shugaban majalisar dokokin kasar Dimitry Rogozin ya ke aikewa shugaba Obama sako cikin barkwanci dangane da hana su taba kadarorinsu inda ya ce to ya za a yi da wadanda ba su da kadara ko kudade a kasashen ketare?

Su kuwa mutane irinsu Sergei Aksenov wanda ke rajin ganin Kirimiya ta balle daga Ukraine cewa ya yi wannan mataki ba zai razana su ko kuma Rasha ba, kuma yau kam wata rana ce ta farin ciki gare su domin kuwa Kirimiya ta koma gida.

A Talatar nan ce shugaban Rasha Vladimir Putin zai yi jawabi ga majalisun dokokin Rasha dangane da halin da ake ciki game da yankin na Kirimiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba

Sauti da bidiyo akan labarin