EU: Bude iyakar Turkiyya ba mafita ba ce | Labarai | DW | 02.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Bude iyakar Turkiyya ba mafita ba ce

Shugabar hukumar zartaswa ta kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce matakin Ankara na bude kan iyakarta ga 'yan gudun hijira su shiga Turai ba shi ne mafita ba.

von der Leyen ta fadi haka ne a yayin da take kalaman tausayawa Turkiyya kan halin da sojojinta ke ciki a yankin Idlib na kasar Siriya. Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na shirin kai ziyara iyakar kasar Girka da Turkiyya, domin daukar matakin kwarar bakin haure.

Girka ta dakatar da shirin ba da mafaka saboda katse dubban 'yan gudun hijira da ke tsallakawa iyakarta daga Turkiyya, bayan da Shugaba Raccep Tayyip Erdogan, ya dauki matakin bude iyakar domin  neman goyon bayan kasahsen kan rikicin Siriya.