Ebola na ci gaba da zama barazana | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ebola na ci gaba da zama barazana

A wannan makon ma dai cutar Ebola da ta yi kamari a wasu kasashen yammacin Afirka ta fi daukar hankalin jaridun na Jamus.

A sharhin da ta rubuta mai taken bala'in da ya mamaye duniya, jaridar Berliner Zeitung cewa ta yi:

"A kullum yaumin labarin kara muni yake yi, inda ma cibiyar yaki da kwayoyin cuta ta Amirka ta yi hasashen cewa idan ba a dauki karin matakan dakile yaduwar cutar cikin gaggawa ba, kafin watan Janerun shekarar 2015, yawan wadanda za su kamu da Ebola yammacin Afirka zai kai tsakanin mutune 550,000 zuwa miliyan 1.4. Jaridar ta ce da yake yanzu ana fuskantar wani bala'i da ke barazana ga duniya baki daya, to mene ne abin yi? Ta dai ba da amsa da cewa: ana bukatar kebabbun wuraren kula da masu fama da cutar cikin hanzari. Kafa irin wadannan wurare kuwa ba ya bukatar wani gagarumin aiki domin cikin kankanen lokaci likitocin kungiyar Medicin Sans Frontier sun samar tantuna masu yawa a kasar Laberiya. Sai dai ana bukatar ma'aikatan kiwon lafiya da za su kula da majinyata. Akwai bukatar kara azama wajen wayar da kan jama'a game da matakan kariya da yadda cutar ke yaduwa."

Fargabar zuwa Afrika saboda Ebola

Naturschutzgebiet Kaza

Namun dawa na daga cikin ababan sha'awa ga 'yan yawon bude ido a Afirka

Tsoron zuwa Afirka inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa annobar cutar Ebola ta yi wa harkokin yawon bude ido a Afirka babbar illa.

Ta ce yanzu haka Ebola ta katse wa 'yan yawon bude ido da ke son zuwa Afirka hanzari, ba ma a kasashen da lamarin ya shafa kadai ba. Tun bayan bullar cutar a yammacin Afirka masu zuwa yawon bude ido a kasashen gabashi da kudancin Afirka suna cikin zullumi. An samu karuwar yawan masu soke tafiya, domin da yawa a cikinsu na daukar Afirka tamkar kasa guda daya, maimakon wata katuwar nahiya da ke kunshe da kasashe mabambamta. Baya ga koma-bayan tattalin arziki da hakan ya janyo wa kasashen Afirka, su ma kamfanonin kasashen Turai da suka kware wajen shirya tafiye-tafiye irin na yawon bude a Afirka suna kokawa game da karancin kudaden shiga, tun bayan bullar cutar Ebola a wasu kasashen Afirka."

Najeriya na tattaunawa da Boko Haram

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon labari ta buga game da wata tattaunawa da ta ce ana yi tsakanin hukumomin Najeriya da kungiyar Boko Haram.

Goodluck Jonathan spricht mit entkommenen Geiseln

Shugaba Jonathan da wasu al'ummar Chibok

Ta ce bisa ga dukkan alamu tun kimanin watanni biyu ke nan gwamnatin Najeriya da kungiyar agaji ta kasa da kasa wato Red Cross suke tattaunawa da kungiyar ta'adda ta Boko Haram da nufin sako 'yan matan makarantar nan kimanin 200 da aka yi garkuwa da su daga garin Chibok tun tsakiyar watan Afrilu. Jaridar ta ce daya daga cikin masu tattaunawar kuma sanannen dan rajin kare hakkin dan Adam a Najeriya wato Fred Eno ya tabbatar da wannan labari. Sai dai kungiyar Red Cross ba ta ce uffan ba game da wannan tattaunawa da ake yi da Boko Haram. Manufar da wannan tattaunawa ta sa gaba shi ne a yi musayar firsinoni kwamandojin Boko Haram da 'yan matan na Chibok wadanda suka kwashe sama da watanni biyar a hannun masu ta da kayar bayan. Jaridar ta ce kawo yanzu gwamnatin Najeriya ta yi watsi da yin musayar firsinoni da kuma 'yan matan da ake garkuwa da su.