Dusar kankara a kasashen Turai | Labarai | DW | 29.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dusar kankara a kasashen Turai

Zubar dusar kankara dai kan sanya murna a zukatan Turawa masu sha'awar wasanni cikin kankara yayin da wasu kuma ta ke zame musu alakakai saboda cikas a harkokin sufuri.

Dusar kankara mai yawan gaske da aka samu tun daga cikin daren jiya Lahadi a tsakanin kasashen Turai ta haifar da rudu da sanya murna a zukatan al'umma da ke zaune a wannan yanki.

Yayin da kimanin mutane dubu 15 ke warwatse a yankunan tsaunika a Faransa cikin wasannin kankara. A Birtaniya yawan dusar kankarar ya haifar daukewar wutar lantarki da zamiyar ababan hawa saboda cikar kankarar a hanyoyin mota a nan Jamus, haka kuma wannan ya haifar da tsaikon ababan sufiri a yankin.

Wani dan Swiss mutum guda ya rasu yayin da wasu talatin suka sami raunika lokacin tafiya a babbar hanya mai tazarar mil 24 daga Ljubljana babban birnin Sloveniya inda kankarar ta zuba sosai a tsakiyar kasar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu