Yan Najeriya 30,000 sun yi kaura zuwa Nijar
June 16, 2020Talla
Syldie Bizimana jami'in majalisar a jamhuriyar Nijar ya ce wannan kaura ta wakana ne a cikin watanni biyu da kauyukan mutanen ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga.
''Mutanen sun samu mafaka a kauyukan Nijar na bakin kan iyaka duk da muna kula da wasu daga cikinsu ba zamu iya karesu ba. Akwai mata da kananan yara a cikin wadannan mutane. Gaskiya sun shiga mawuyacin hali.'' inji Mista Bizimana.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da suka yi kaura zuwa Nijar a baya-bayan nan sun fito ne daga jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto. Majalisar ta ce kashe-kashe da garkuwa da mutane gami da hare-hare babu kakkautawa suka tilastawa mutanen barin gidajensu don tsira da rayuwarsu.