Dubban ′yan gudun hijira sun isa birnin Munich na Jamus | Labarai | DW | 02.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban 'yan gudun hijira sun isa birnin Munich na Jamus

Al'ummar wannan yanki na dauke da kwalaye da ke da rubutu wanda ke cewa " 'Yan gudun hijira muna muku lalale marhabun".

Deutschland Flüchtlinge München Hauptbahnhof

'Yan gudun hijira a birnin Munich

A kalla 'yan gudun hijira 3,500 ne suka isa jihar Bavaria da ke a kudancin Jamus cikin kwanaki biyun baya-bayan nan da masu neman mafaka ke kwarara zuwa Turai.

Da dama cikin 'yan gudun hijira sun sauka ne a tashar jirgin kasa da ke a Munich inda suka sami tarba ta musamman ta al'ummar wannan yanki wadanda ke dauke da kwalaye dauke da rubutu wanda ke cewa " 'yan gudun hijira muna muku lalale marhabun". Mahukunta a wannan kasa dai sun bayyana cewa suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun tallafa wa wadannan mutane da suka sami kansu cikin hali na tsananin bukata.

Kasar dai ta Jamus na zama kasa ta farko da dubban 'yan gudun hijira daga kasashen Gabas ta Tsakiya da Afirka ke son su dangana da ita inda a cikin wannan shekara ta 2015 kasar ke tsammanin yawan 'yan gudun hijira da za su nemi mafakar siyasa su kai 800,000.

A wani labarin kuma akwai dubban 'yan gudun hijira da suka tsinci kai cikin hali na tsaka mai wuya bayan da 'yan sanda a Hungary suka hana musu damar ketara iyaka zuwa Ostiriya daga nan zuwa Jamus.