Dubban mutane na tserewa daga Afrin
March 21, 2018Talla
Mai magana da yawun gwamnati Ulrike Demmer ta ce, su na bin diddigin rahotannin yadda Turkiyyar ta kwace mafi yawan garuruwan da ke yankin, kuma abun takaici ne yadda dubban mutane ke tserewa domin neman mafaka saboda halin da ake ciki a birnin na Afrin.
Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen na Jamus ta yi kira da a gudanar da binciken rahotannin irin kisan kiyashi da dibar ganima da ke gudana a Afrin, tare da hawa teburin sasanta wannan rikici da Siriya.
Dubban 'yan gudun hijira ne dai ke cigaba da ficewa daga garin wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne, saboda kazamin fada da ake gwabzawa.