Dortmund ta kori mai horas da 'yan wasanta
December 10, 2017Kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ta kasar Jamus ta kori mai horas da 'yan wasanta Peter Bosz a wannan Lahadi tare da maye gurbinsa da Peter Stöger tsohon mai horas da 'yan wasan Kungiyar Köln wanda kungiyarsa ta kora a makon da ya gabata.
Shugaban kungiyar Hans-Joachim Watzke ne ya sanar da hakan jim kadan bayan wani taron gaggawa da kungiyar ta kira a wannan Lahadi. Wannan mataki ya zo ne kwana daya bayan kashin da kungiyar ta Dortmund ta sha a gida da ci biyu da daya a jiya Asabar a gaban Kungiyar Werder Brem wacce ke a matsayin ta 17 a tebirin Bundesliga.
Bayan wasannin mako na 15 na Bundesliga, Kungiyar Dortmund wacce ta sha lashe gasar ta Bundesliga da daukar kofin zakarun Turai a shekarun baya na a matsayin ta bakwai a halin yanzu da maki 22 kacal a tebirin na Bundeliga.
Nadin Peter Stöger sabon mai horas da 'yan wasan Kungiyar ta Dortmund ya zo ne mako daya bayan da Kungiyar Köln ta sallama shi a bisa rashin kyakyawan sakamako inda kungiyar ta kasance a matsayin ta karshe a tebirin na Bundesliga da maki uku kawai bayan wasanni 14.