Cin hanci ya karu fiye da kima a duniya - Transparency
February 10, 2026
A rahotonta na shekara-shekara da ta fitar kungiyar Transparency International ta ce cin hanci da rashawa ya karu matuka a duniya, lamarin da ke zama mafi muni a cikin shekaru 10.
Kungiyar mai mazauni a birnin Berlin na Jamus ta ce akwai babbar fargaba a Amurka duba da yadda ake yin dirar mikiya kan masu karfin fada a ji abin da kuma ke yin babbar illa ga tafiyar da fannin shari'a.
Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin yaki da cin hanci a Ukraine, kasar da a baya ta yi kaurin suna wajen wannan haramtacciyar dabi'a.
A cikin shekaru takwas a jere kasar Denmark ce ke kan gaba wajen rashin aikata dabi'ar cin hanci, inda ta samu maki 89.
Transparency Internationl ta kuma soki kungiyar Tarayyar Turai kan yadda da zuba ido ta kyale ana murdewa dimokuradiyya wuya a wasu gwamnatocin kasashe membobinta ba ta tare da yin amfani da matakan da suka dace ba don takawa wannan mummunar dabi'a birki.