Dangantaka tsakanin Sudan da Chadi na kara yin tsami | Labarai | DW | 01.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantaka tsakanin Sudan da Chadi na kara yin tsami

Sudan ta umarci sojojin Chadi dake yiwa kungiyar tarayyar Afirka aikin sa ido kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a Darfur da su fice daga yankin. Kakakin kungiyar AU Noureddine Mezni ya ce yanzu haka dukkan wakilan Chadi su kimanin mutum 30 sun hallara a garin el-Fasher na arewacin Darfur kuma nan ba da dadewa ba zasu fice daga wannan yanki. Mezni ya ce sun yi bakin ciki da wannan mataki da gwamnatin Sudan ta dauka, sannan ya yi kira ga sassan biyu da su fara tattaunawa don warware banbancen dake tsakanin su cikin lumana. A halin da ake ciki dai dangantaka tsakanin Cahdi da Sudan ta tabarbare inda kowacen su ke zargin daya da taimakawa ´yan tawaye.