Matasan yankin Sahel da suka rungumi salon kidan Hip-Hip sun sake baje basirar da Allah ya yi musu a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar. Wannan shi ne karo na biyar da mawakan na kasashen Afirka ta yamma suka shirya wannan biki, amma a wannan karon sun mayar da hankali kan illar da ke tattare da ratsa hamadar sahara don zuwa cin rani a kasashen Turai ta barauniyar hanya.