1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani ya kai hari da babbar mota a Jamus

Abdul-raheem Hassan
October 8, 2019

Akalla mutane tara ne suka jikkata bayan da wani mahari ya bi ta kan motoci a garin Limburg da ke yammacin Jamus. Ana zargin mutumin ya saci babbar motar da ya kai harin da ita ne.

https://p.dw.com/p/3QtJd
Deutschland Limburg Lastwagen rammt Fahrzeuge
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Ditschner

Jami'an tsaro a yankin Limburg sun tabbatar da cewa maharin dan asalin kasar Siriya ne da ke neman mafaka a Jamus, sai dai hukumomi na ci gaba da binciken musabbin harin ko yana da alaka da ta'addanci. A shekarar 2016 ma wani dan gudun hijirar kasar Tunisiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu 70 yayin da ya bi ta kan mutane da babbar mota a kasuwar kirsimeti a Berlin fadar gwamnatin Jamus.