1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: Jamus ta tsawaita dokar zaman gida

Ramatu Garba Baba
April 16, 2020

Gwamnatin Jamus ta ce za ta tsawaita dokar da ta sanya don hana yaduwar cutar Coronavirus ya zuwa watan gobe, za a bude makarantu da zarar wa'adin ya cika, amma daga ranar Litinin mai zuwa za a soma bude kananan shaguna.

https://p.dw.com/p/3ayLj
Coronavirus Frankreich Mülhausen medizinisches Personal transportiert Patienten
Hoto: AFP/S. Bozon

Gwamnatin Jamus ta ce za ta tsawaita dokar da ta sanya don hana yaduwar cutar Coronavirus ya zuwa uku ga watan gobe, za a bude makarantu da zarar wa'adin ya cika, amma daga ranar Litinin mai zuwa za a soma bude kananan shaguna, za a kuma ci gaba da rufe iyakokin kasar, a yayin da dokar hana taron jama'a da yawa za ta ci gaba da aiki ya zuwa karshen watan Augustan wannan shekarar da muke ciki.

Mutum sama da dari shida ne aka gano suna dauke da cutar numfashi ta Covid-19 a Faransa, suna daga cikin ma'aikatan jirgi fiye da dubu daya da dari biyar da aka yi wa gwajin cutar a wannan Laraba, akwai fargabar alkaluman ka iya karuwa ganin yadda suka yi cudanya da juna. Ma'aikatan jirgin ruwa 668 daga cikin sama da dubu daya da aka yi wa gwaji na dauke da cutar Coronavirus a Faransa, a yayin da cutar ta halaka mutum fiye da dubu dari a kwana guda a sassan duniya.

A Turkiyya, mutum fiye da dari biyu Coronavirus ta halaka, inda kusan kullum ake samun mutuwar mutum dari, yanzu haka an samu karin mutum sama da dubu hudu da cutar ta kama a kwana guda. Kawo yanzu Covid-19 ta yi sanadiyar rayuka sama da dubu daya da dari biyar a kasar. Tuni gwamnatin Ankarar ta karfafa matakan hana yaduwar cutar da suka hada da rufe makarantu da taron jama'a.

Mutum fiye da dubu dari da talatin Coronavirus ta kashe a wannan Laraba a yayin da adadin wadanda cutar ta kama suka doshi miliyan biyu tun bayan bullarta a Disambar bara.