1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus na kara bunkasa, inji WHO

February 28, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar a ranar Jumma'a cewa Coronavirus na ci gaba da bunkasa a duniya. Bayanin ya zo bayan Najeriya ta sanar da bullar cutar a karon farko a jihar Lagos.

https://p.dw.com/p/3YbMu
Coronavirus  Mexiko PK Pressekonferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Solis

Mai Magana da yawun Hukumar Christian Lindmeier ya shaida wa 'yan jarida a birnin Geneva cewa da alama cutar na da karfin mamaye kusan kasashen duniya. 
A gefe guda kuma kwamishinan lafiya na jihar Legas ta Najeriya  Akin Abayomi ya ce dan kasar Italiya da aka samu da Coronavirus a Najeriya ya fara ratsowa ta kasar Turkiyya, a sa'ilin da ya iso Najeriya kuma sai da ya yada zango a jihar Ogun kafin daga karshe a gano yana dauke da cutar a wani asibitin da ke unguwar yaba ta birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriya.