1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta tanadin kayan gwajin mutum 500,000

March 26, 2020

Gwamnatin Jamus ta sanar a wannan Alhamis cewa ta yi tanadin kayan aiki da za ta iya yi wa mutum akalla 500,000 gwajin cutar Corona a cikin mako guda.

https://p.dw.com/p/3a4Xw
Deutschland PK Coronavirus Angela Merkel Kontaktverbot
Hoto: Reuters/M. Kappeler

Christian Drosten babban jami'i da ke jagorantar cibiyar nazarin cututtuka nau'in Virus da ke birnin Berlin shi ne ya bayar da wannan tabbaci.

Masanin ya ce kokarin yin gwaji da Jamus ke yi shi ne yasa duk da cewa kasar tana ci gaba da samun karuwar masu Corona amma kuma cutar ba ta yin kisa sosai idan an kwatanta da sauran kasashe. Kawo yanzu dai mutane 37,300 ke dauke da Coronavirus din a cikin Jamus.

Wannan labarin na zuwa ne a daidai lokacin da a safiyar Alhamis din nan wani bincike ya nuna cewa akasarin Jamusawa sun nuna gamsuwa a kan yadda gwamantin Angela Merkel ke daukar matakan dakile yaduwar cutar Corona a kasar.