COP 23: Taro kan sauyin yanayi a Bonn | Zamantakewa | DW | 09.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

COP 23: Taro kan sauyin yanayi a Bonn

A wannan makon ne aka bude taron duniya kan sauyin yanayi karo na 23 da nufin tunatar da wakilan kasashen duniya irin bala'in da sauyin na yanayi ke haifarwa don daukar matakan magance su.

Yayin da aka fara muhawa kan dumamar duniya a babban taron na kasa da kasa kan sauyin yanayin da ke gudana a birnin Bonn na Jamus, Firaministan Fiji da ke jagorantar taron karon na 23 ya tunasar da mahalarta taron da suka fito daga kasashe fiye da 190, da su yi la'akari da bala'in da sauyin yanayin yake haifarwa domin cimma matsaya ta daukar matakan bai daya don magance matsalar. 

Taron wanda aka bude cikin armashi da annashuwa tare da kade kade da raye raye na al'adun al'ummar Fiji ya ja hankali ga bukatar wanzar da cigaba mai dorewa a duniya. Shugaban taron kuma Firaministan kasar ta Fiji Frank Bainimarama ya nuni da yadda iftila'in ambaliyar ruwa ta kassara yar karamar kasar ta tsibirin kudancin Pacific sakamakon sauyin yanayi.

A kokarinta na tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Paris, gwamnatin Jamus ta ce ba gudu ba ja da baya akan wannan yarjejeniya, abin da ke zama martani ga matakin shugaban Amirka Donald Trump na janye kasarsa daga yarjejeniyar idan kasar ba ta sami masalaha mafi dacewa a gare ta ba.

Ministar muhalli ta Jamus Barbara Hendricks, ta bukaci mahalarta taron su san da cewa akwai bukatar hada karfi da karfe domin tabbatar da cimma matsaya kan jadawalin aiwatar da yarjejeniyar ta Paris.

DW.COM