Bonn: An yi zanga-zanga kan kare muhalli | Labarai | DW | 04.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bonn: An yi zanga-zanga kan kare muhalli

Dubban mutane ne suka shiga wata zanga-zanga da aka gudanar a wannan Asabar din a birnin Bonn na tarayyar Jamus inda aka rika kira ga hukumomi kan su dau matakai na kare muhalli.

Wadanda suka gudanar da zanga-zangar sun hada da masana da kungiyoyi na masu rajin kare muhalli daban-daban. Zanga-zangar na zuwa ne a yayin da ake shirin soma taron kasashen duniya kan sauyin yanayi na duniya wato COP23, taron da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya zai gudana a nan birnin Bonn inda za a kwashe kwanaki 12 ana gudanar da shi. Akalla mutane daga kasashe duniya 196  za su halarci wannan taron da zummar yin nazari kan magance wannan matsalar dumamar yanayi.