COP23: An fara taro kan sauyin yanayi a birnin Bonn | Labarai | DW | 06.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

COP23: An fara taro kan sauyin yanayi a birnin Bonn

A yau Litinin ne aka bude taron duniya kan sauyin yanayi  a nan Bonn na tarayyar Jamus inda mahalarta za su yi nazarin illolin da gurbatar yanayin ke yi wa kasashen duniya.

Taron wanda za a dauki kwanaki 12 ana yi, na da wakilai dubu 25 ne daga sassa daban-daban. Kasashe 196 ke da wakilci lokacin taron na birnin Bonn. A bara ne dai kasashe suka hadu a birnin Paris na kasar inda suka cimma yarjejeniyar daukar kwararan matakan maganta bazanar sauyin yanayin da aka hakikance cewa manyan masana'antu na zamani na daga ciki.