COP23: An bukaci hadin kan kasashen duniya | BATUTUWA | DW | 06.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

COP23: An bukaci hadin kan kasashen duniya

Firaministan Fiji da ke jagorantar taro kan Sauyin yanayi a Jamus, ya tunasar da mahalarta taron da su yi la'akari da bala'in da lamarin ke haifarwa domin cimma matsaya ta daukar matakan bai daya don magance matsalar.

Taron wanda aka bude cikin armashi da annashuwa tare da kade-kade da raye raye na al'adun al'ummar Fiji ya ja hankali ga bukatar wanzar da ci gaba mai dorewa a duniya. Shugaban taron kuma Firaministan kasar Fiji Frank Bainimarama ya yi nuni da yadda iftila'in ambaliyar ruwa ta kassara 'yar karamar kasar ta tsibirin kudancin Pacific sakamakon sauyin yanayi, ya kara da cewa yana gabatar da sako daga Fiji da yankin Pacific da kuma kasashe masu rauni na duniya cewa lamarin fidda yawan gurbataccen hayaki ya isa hakan nan tare da bukatar duniya ta dauki mataki kafin ruwa ya ci kasarsu baki daya.

COP23 UN Klimakonferenz in Bonn Eröffnung (Reuters/W. Rattay)

Firaministan Fiji Frank Bainimarama da ke jagorantar taron COP23

A kokarinta na tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Paris, gwamnatin Jamus ta ce ba gudu ba ja da baya akan wannan yarjejeniya, abin da ke zama martani ga matakin shugaban Amirka Donald Trump na janye kasarsa daga yarjejeniyar idan kasar ba ta sami masalaha mafi dacewa a gare ta ba. Ministar Muhalli ta Jamus Barbara Hendricks ta bukaci mahalarta taron cewa akwai bukatar hada karfi da karfe domin tabbatar da cewa an cimma matsaya kan jadawalin aiwatar da yarjejeniyar ta Paris.

Deutschland Pk zum Weltklimagipfel in Bonn

Ministar Muhalli ta Jamus Barbara Hendricks

Tuni dai sauran kasashe fiye da 160 da suka rattaba hannu akan yarjejeniyar suka ce za su ci gaba da yunkurinsu na tabbatar da yarjejeniyar ta rage dumamar duniya. Amman kuma wani babban jami'in diplomasiyyar Amirka da ya halarci taron Trigg Talley kuma jakadan Amirka na musamman kan sauyin yanayi ya ce matsayin Amirkar bai sauya ba tun bayan da Trump ya yi wannan furuci a watan Yuni. A waje guda dai hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce wannan shekarar ita ce mafi tsananin zafi da aka fuskanta tsawon shekaru uku a jere. A makon karshe na taron ana sa ran halartar shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran shugabanni na duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin